An haifeshi a birnin madina shekarata 26h’ bayan an zowa da Imam Ali As busharar haihuwarsa yayi saurin zuwa gida ya dauke shi ya sumbace shi yana mai farinciki ya gudanar masa da dukkan abinda sharia ta tanada da akewa jarirai bayan Haihuwarsu.
Ya rayu karkashin kulawar mahaifinsa na tsawon shekarau 14 kane ne shi ga Imam Husain As wanda ya shahara da Jarumtarsa da dakewarsa wanda ya Nuna a lokacin Waki’ar Karbala inda suka tafi debo ruwa tare da Imam Husain As kamar yadda Shaikul Mufid ya kawo amma sai sojojin Umar dan Sa’ad suka raba tsakaninsa da Imam Husain As Inda suka zagaye shi amma duk da hakan ya yakesu shi kadai har saida ya fadi kasa daga kan dokinsa inda suka yanke masa Hannayensa biyu daga karshe suka Shahadantar da shi a lokacin da yayi shahada yana dan shekara 34 ne As.
Your Comment